Featured
Musulmi 75 Aka Kashe a Hare-haren Woro da Nuku – Gwamnan Kwara

Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya ce musulmi 75 ne aka kashe a hare-haren da aka kai al’ummomin Woro da Nuku. Ya bayyana cewa masu tsattsauran ra’ayin addini ne suka kai harin, ba ‘yan bindiga ba.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X bayan ziyarar da ya kai yankin a daren Laraba. Ya ce Shugaba Bola Tinubu ya tura bataliyar sojoji jihar Kwara domin mayar da martani da kuma ƙarfafa tsaro.
Hukumomin Najeriya sun ɗora alhakin harin kan ƙungiyar Boko Haram, yayin da fadar shugaban ƙasa ta la’anci abin da ta kira mummunan hari na rashin imani. Amnesty International ta nemi a gudanar da bincike mai zaman kansa, yayin da aka kuma ambaci wasu hare-haren da suka faru a jihohin Neja, Kogi da Katsina.