Connect with us

Featured

Masu Garkuwa Da Mutane Sun Sake Kai Hari Kwara

An sake fuskantar tashin hankali a Isapa, kusa da Eruku, a Karamar Hukumar Ekiti ta jihar Kwara, inda akalla mutum 11 aka yi garkuwa da su. Lamarin ya faru da misalin ƙarfe 6:00 na yamma a ranar Litinin, 24 ga Nuwamba 2025, kwanaki guda bayan sako wasu da aka sace a coci. Shaidu sun ce maharan sun isa garin suna harbi, abin da ya sa mazauna yankin tserewa don tsira.

Wadanda aka sace sun haɗa da mata masu juna biyu, iyaye masu shayarwa, da kananan yara, har ma da gida ɗaya da aka kwashe mutane bakwai. Sunayen waɗanda aka ɗauke sun haɗa da Talatu Kabiru (20), Magaji (6), Kande (5), Hadiza (10), Mariam (6), Saima (5), da wasu mata biyu — Habibat da Fatima Yusufu. Sauran su ne Sarah Sunday (mai juna biyu), Lami Fidelis (23) da Haja Na Allah, wadanda dukkaninsu ke cikin halin damuwa. Shaidu sun ce bayan maharan sun bar yankin, an tarar da kwararan harsashin AK-47 a wurare dabam-dabam.

A yanzu damuwa ta karu a cikin Isapa da kauyukan dake makwabtaka, yayin da jami’an tsaro da ƙungiyoyin vigilante ke ƙoƙarin gano inda aka tafi da mutanen. Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, Kwamishina Adekimi Ojo, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa yana kan hanyarsa ta zuwa Isapa don tantance abin da ya faru. Kakaki24 ta gano cewa wannan mummunan lamari na zuwa ne a daidai lokacin da matsalar tsaro ke taɓarɓarewa a fadin Najeriya.

Rahotanni na nuna cewa rikice-rikicen tsaro sun jefa makarantu da dama a arewacin ƙasar cikin rufewa tare da tsaida harkokin yau da kullum. Al’ummar yankin na kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su hanzarta ɗaukar matakai domin ceto waɗanda aka sace da kuma kawo ƙarshen hare-haren da suka zame musu ruwan dare.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahistipobettipobetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobettipobetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet