Featured
Kimanin Mutane 5 Ne Suka Mutu Sakamakon Maƙalewa a Rijiya a Kano

Aƙalla mutane biyar ne suka rasa rayukansu a wasu munanan lamurra da suka faru a kananan hukumomin Bichi, Danbatta da Nassarawa na Jihar Kano. A Badume Kanawa, Bichi, mutum uku sun mutu bayan igiyar da suke amfani da ita wajen gyaran rijiya ta yanke, inda Sa’idu Gada, Sani Isyaku, da Yakubu Abdullahi suka shiga ramin domin ceton juna, amma dukkansu suka makale. Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta tabbatar da faruwar lamarin.
Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Saminu Abdullahi, ya ce ma’aikatansu sun isa wurin inda suka tarar da mutanen uku a cikin rijiyar, nan take aka ciro su sun fita a hayyacinsu, daga bisani aka tabbatar da rasuwarsu. Kuma tuni aka mika gawarwakin ga ’yan sandan Badume.
A wani lamarin daban a Danbatta, Saminu Abdullahi ya tabbatar da rasuwar wani yaro dan kimanin shekara 10, Hassan Iliyasu Haruna, wanda ya fada rijiya ya mutu.
A Nassarawa Local Government, Badawa Layin Day, wata yarinya ’yar shekara 10 ta mutu a gobarar da ta tashi a ranar Alhamis, 4 ga Disamba 2025. Hukumar kashe gobarar ta ce da suka isa wurin, gobarar ta riga ta cinye dakuna biyu, duk da na ciro yarinyar bata mutu ba, amma daga bisani tace ga garinku nan daga bisani tace ga garinku nan.
A jawabin da ya yi, Daraktan hukumar, Sani Anas, ya ja kunnen jama’a da su daina tsalle cikin rijiya domin ceto wani da ya makale, yana mai cewa hakan na janyo ƙarin mace-mace. Ya yi kira da a kira jami’an hukumar ko da yaushe a irin waɗannan lokuta domin guje wa asarar rayuka.