Featured
Kotu Ta Tsare Malamin Jami’a Da Ya Zargi Gwamnatin Katsina Da Bai Wa Ƴan Bindiga Kujerun Aikin Hajji

Wata Kotun Majistare da ke Katsina ta ba da umarnin tsare Dr. Bashir Kurfi, malami a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, bayan ‘yan sanda sun gurfanar da shi kan zargin bata suna da yada bayanan karya masu cutarwa ga gwamnatin jihar.
Ana zargin Dr. Kurfi ya yi ikirarin a wata hira da Trust TV cewa Gwamnatin Jihar Katsina ta dauki nauyin aikin Hajjin wasu shugabannin ‘yan bindiga. Sai dai ya musanta zargin bayan an karanta masa tuhume-tuhumen, yayin da lauyansa ya nemi a bayar da belinsa
Kotun ta umarci a ci gaba da bincike tare da tsare wanda ake zargin har zuwa ranar 14 ga Yulin 2026 domin ci gaba da shari’ar. Bayan zaman kotun, lauyansa ya bayyana kwarin gwiwar cewa za a wanke shi daga zarge-zargen da ake masa.