Featured
An saki Alƙalin Babbar Kotun Kebbi da aka yi garkuwa da shi

An saki Alƙalin Babbar Kotun Jihar Kebbi, Justice Faruku Bunza, wanda aka yi garkuwa da shi mako guda da ya gabata a Ƙaramar Hukumar Bunza.
A cikin wata sanarwa da rundunar ’yan sandan jihar ta fitar, mai magana da yawunta, Bashir Usman, ya ce an tabbatar da sakin alƙalin a ranar Litinin, inda iyalansa da Ma’aikatar Shari’a ta jihar suka tabbatar da komawarsa gida cikin ƙoshin lafiya.
Rundunar ’yan sandan ta ce duk da cewa masu garkuwar sun nemi a biya kuɗin fansa, ba a biya su ko sisi ba kafin sakin alƙalin.
Ta kuma bayyana cewa jami’an tsaro na ci gaba da bincike domin gano tare da kama mutanen da ke da hannu a sace alƙalin, domin su fuskanci hukunci a gaban doka.