Connect with us

Featured

Majalisar Dokokin Kano ta dakatar da shugabannin ƙananan hukumomin Bagwai, Bebeji da Rogo na tsawon watanni uku

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta dakatar da shugabannin ƙananan hukumomin Bagwai, Bebeji da Rogo daga bakin aiki na tsawon watanni uku. Jami’in Yaɗa Labaran Majalisar, Malam Kamaluddeen Sani Shawai, ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai.

Ya ce matakin ya biyo bayan karɓar rahoton kwamitin da majalisar ta kafa domin binciken ƙorafe-ƙorafen da ƙungiyoyi da al’ummomin ƙananan hukumomin suka shigar kan shugabanninsu.

Read Also : Malamin da ya shiga siyasa aka dama da shi ya fi malamin da ya zauna yana yi wa ƴan siyasa addu’a – Sheikh Gumi

A cewar jami’in, ƙorafe-ƙorafen sun shafi zargin badaƙalolin almundahana da kuɗaɗen al’umma. Ya ce majalisar ta ɗauki matakin ne bayan samun rahoton kwamitin da aka kafa domin binciken lamarin.

Shugabannin da aka dakatar sun haɗa da Alhaji Bello Abdullahi Gadanya na Bagwai, Dr. Alhassan Salisu na Bebeji da Alhaji Abubakar Mustapha Rogo na Rogo, domin ba da damar gudanar da cikakken bincike kan zarge-zargen.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet