Featured
An ƙaddamar Da Kundin Buƙatun Abubuwan Da Arewacin Najeriya Ke Bukata Ga ƴan Takarkaru

Gamayyar ƙungiyoyin cigaban matasan arewacin Najeriya ta gudanar da taron ƙaddamar da kundin bukatun arewacin Najeriya ga yan takara daga kowanne mataki, tare da ƙaddamar da Co-odinetocin ƙungiyar na jahohi 19 ciki har da birnin tarayya Abuja.
Wasu daga cikin Coordinators na ƙungiyoyi
Taron wanda ya gudana a ranar Asabar ɗin da ta gabata 11 ga watan faburairun 2023, a dakin taro dake masallacin Ahmadu Tijjani dake Ƙofar Mata a jihar Kano.
Wasu Daga Cikin Mahalarta Taron
Karƙashin jagoranci shugabar ƙungiyar ta ƙasa Malama Fatima Tasallah Nabulisi Baƙo MFR.
Jaridar Kakaki Hausa ta rawaito cewa shugabar Ƙungiyar ta ƙasa Malama Tasalla tace, duk ɗan takarar da ya samu dama a zaɓe mai zuwa a 2023, bai aiwatar da waɗannan ƙudurori da suka gabata ba, to babu shakka idan ya dawo a kawo ba gaba zai sha mamaki.
Taron ya samu halartar manyan baƙi da kuma ƴan takarkaru a matakai daban daban.
Wasu daga cikin manyan baƙi
Cikin waɗanda suka halarci taron akwai ɗan takarar gwamna a jam’iyyar PRP Salihu Tanko Yakasai, da na jam’iyyar ADC Malam Ibrahim Khalil, sai na jam’iyyar ADP Sha’aban Ibrahim Sharada.
Sauran sun haɗa da wakilin ɗan takarar gwamna a jam’iyyar APC kuma mataimakin gwamnan Kano Nasiru Yusif Gawuna, wanda ya samu wakilcin Alh. Abba Tage, sai wakilin ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar PDP Atiku Abubakar wazirin Adamawa.
Kaɗan daga cikin abin da kundin ya ƙunsa sun haɗa da yadda za’a magance matsalar tsaro da inganta harkar ilimin da cigaban matasa da kuma haɓɓaka harkar noma da fannin ilimin na’ura mai ƙwaƙwalwa (Technology) sai gyaran hanyoyi da dai sauransu.