Connect with us

Featured

Zulum Ya Sha Alwashin Hukunta Ma’auratan Da Suka Ci Zarafin Wata Yarinya

Gwamnatin jihar Borno, ta ɗauki matakin hukunta wasu ma’aurata, Mamman Sheriff da matarsa, da aka kama suna cin zarafin wata yarinya a unguwar Pompomari Bypass da ke Maiduguri.

Bayan bayyanar faifan bidiyon da ya nuna ma’auratan suna dukan yarinyar, mutane da dama sun yi tir da abin a shafukan sada zumunta.

Wannan ya sa Hukumar kula da kadarorin gwamnati da tsaron al’umma Sibil Difens (NSCDC) ta cafke su nan take.

Gwamnan jihar, Babagana Umara Zulum, ya tabbatar da cewa gwamnati ba za ta musu sassauci ba.

Ya ce ma’aikatun shari’a, ilimi, da harkokin mata sun haɗa kai domin ganin an hukunta waɗanda suka aikata laifi.

Yarinyar, wacce ɗaliba ce, ta shiga harabar gidan ma’auratan domin tsinkar mangwaro bayan tashi daga makaranta, inda suka yi mata dukan kawo wuƙa.

A halin yanzu tana kwance a asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri (UMTH), inda Dokta Lawan Bukar Alhaji ya ɗauki nauyin jinyarta.

Gwamnatin Borno ta kuma tallafa wa iyayen yarinyar da kayan agaji, abinci, da kuɗi.

Iyayenta da sauran jama’a sun yaba wa gwamnatin kan matakin da ta ɗauka na kare haƙƙin yarinyar.

Gwamnati ta jaddada cewa duk wanda aka kama da cin zarafin yara ba zai tsira daga hukunci ba.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet